Skip to content
Mattiyu 23:23-28

Mattiyu 23:23-28

23
“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.
24
Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.
25
“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai.
26
Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta.
27
“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.
28
Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options