Mattiyu 17:7-20
7
Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
8
Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.
9
Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”
10
Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?”
11
Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.
12
Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”
13
Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.
14
Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa.
15
Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa.
16
Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”
17
Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”
18
Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
19
Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”
20
Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
Settings