Mattiyu 17:1-8
1
Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.
2
A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.
3
Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
4
Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”
5
Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”
6
Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice.
7
Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
8
Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.
Settings