Markus 9:27-33
27
Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
28
Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”
29
Ya amsa ya ce, “Sai da addu’akaɗai irin wannan yakan fita.”
30
Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba,
31
gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”
32
Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
33
Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”
Settings