Markus 6:7-13
7
Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.
8
Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku.
9
Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.
10
Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin.
11
In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”
12
Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba.
13
Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
Settings