Markus 15:16-24
16
Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.
17
Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.
18
Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”
19
Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a.
20
Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
21
Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.
22
Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).
23
Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.
24
Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.
Settings