Markus 14:53-58
53
Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.
54
Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.
55
Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.
56
Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
57
Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,
58
“Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ”
Settings