Markus 13:33-37
33
Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba.
34
Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.
35
“Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne.
36
In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci.
37
Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”
Settings