Skip to content
Luka 3:1-6

Luka 3:1-6

1
A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.
2
A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.
3
Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.
4
Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.
5
Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.
6
Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options