Skip to content
Luka 23:26-33

Luka 23:26-33

26
Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.
27
Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makoki da kuka dominsa.
28
Yesu ya juya, ya ce musu, “’Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ’ya’yanku.
29
Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’
30
Sa’an nan “ ‘za su ce wa duwatsu, “Ku fāɗi a kanmu!” Za su ce wa tuddai kuma, “Ku rufe mu!” ’
31
Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?”
32
Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye.
33
Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options