Skip to content
Luka 22:47-53

An Kama Yesu

Luka 22:47-53

An Kama Yesu

47
Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don yă yi masa sumba.
48
Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”
49
Da masu bin Yesu suka ga abin da zai faru, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takubanmu ne?”
50
Sai ɗayansu ya kai sara ga bawan babban firist, ya sare kunnen damansa.
51
Amma Yesu ya amsa ya ce, “Kada a ƙara yin wannan!” Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi.
52
Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, da dattawa, waɗanda suka zo don su kama shi, “Ina jagoran wani tawaye ne, da za ku zo da takuba da sanduna?
53
Kullum ina tare da ku a filin haikali, amma ba ku kama ni ba. Amma wannan ne sa’a naku, lokacin da duhu yake mulki.”

Nazarin nassin nan

Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Yohanna 18:11

    Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”
    daga aya ta 47
  • Yohanna 18:10

    Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.)
    daga aya ta 50
  • Luka 22:4

    Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.
    daga aya ta 52
  • 2 Sama’ila 20:9

    Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba.
    daga aya ta 48
  • 2 Sama’ila 20:10

    Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.
    daga aya ta 48
  • Markus 14:44

    Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.”
    daga aya ta 48
  • Markus 14:46

    Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.
    daga aya ta 48
  • Karin Magana 27:6

    Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
    daga aya ta 48
  • Markus 14:47

    Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.
    daga aya ta 50
  • Luka 22:38

    Almajiran suka ce, “Duba Ubangiji, ga takuba biyu.” Yesu ya ce, “Ya isa.”
    daga aya ta 49
  • 2 Korintiyawa 10:4

    Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.
    daga aya ta 50
  • Mattiyu 26:51

    Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.
    daga aya ta 50
All Luke Sites (Jerusalem)
All Luke Sites (Jerusalem) View full PDF
All Luke Sites (Levant)
All Luke Sites (Levant) View full PDF
All Luke Sites (Eastern Mediterranean)
All Luke Sites (Eastern Mediterranean) View full PDF

Map © Biblica Open Bible Maps · CC BY-SA 4.0

Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options