Luka 19:35-40
35
Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai.
36
Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.
37
Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,
38
“Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”
39
Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”
40
Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”
Settings