Firistoci 7:23-27
23
“Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Kada ku ci wani kitsen shanu, ko na tumaki, ko kuwa na awaki.
24
Za a iya yin wani amfani da kitsen dabbar da ta mutu mushe, ko kitsen dabbar da namun jeji su yayyaga, amma kada a kuskura a ci.
25
Duk wanda ya ci kitsen dabbar da aka miƙa ta wuta ga Ubangiji, za a fid da shi daga mutanensa.
26
Kuma duk inda kuke zama, ba za ku ci jinin wani tsuntsu ko na dabba ba.
27
Duk wanda ya ci jini, za a fid da mutumin daga mutanensa.’ ”
Settings