Tsallake zuwa abun ciki
Firistoci 24:15-23

Firistoci 24:15-23

15
Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa,
16
duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.
17
“ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
18
Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai.
19
Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi;
20
karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa.
21
Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
22
Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
23
Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options