Skip to content
Firistoci 24:17-23

Dokokin Ramuwar Gayya da Adalci

Firistoci 24:17-23

Dokokin Ramuwar Gayya da Adalci

17
“ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
18
Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai.
19
Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi;
20
karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa.
21
Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
22
Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
23
Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Duba kuma

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Fitowa 12:49

    Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”
    daga aya ta 22
  • Maimaitawar Shari’a 19:11

    Amma idan wani mutum yana ƙin maƙwabcinsa, ya kuma yi kwanto yana fakonsa, ya yi masa rauni, har ya kashe shi, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane,
    daga aya ta 17
  • Maimaitawar Shari’a 19:12

    dattawan garinsa za su aika a kawo shi, a dawo da shi daga birnin, a miƙa shi ga mai neman fansar jini don yă kashe shi.
    daga aya ta 17
  • Farawa 9:5

    Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.
    daga aya ta 17
  • Farawa 9:6

    “Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.
    daga aya ta 17
  • Ƙidaya 9:14

    “ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”
    daga aya ta 22
  • Ƙidaya 15:15

    Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.
    daga aya ta 22
  • Ƙidaya 15:16

    Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ”
    daga aya ta 22
  • Firistoci 24:21

    Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
    daga aya ta 18
  • Maimaitawar Shari’a 19:21

    Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.
    daga aya ta 19
  • Mattiyu 5:38

    “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’
    daga aya ta 19
  • Firistoci 19:34

    Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
    daga aya ta 22
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options