Makoki 4:1-10
1
Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna.
2
Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane!
3
Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.
4
Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su.
5
Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka.
6
Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.
7
’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.
8
Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace.
9
Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona.
10
Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena.
Settings