Skip to content
Mahukunta 5:3

Mahukunta 5:3

Ana nuna aya 3 tare da mahallin da ke kewaye.
1
A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.
2
“Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora, sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu, suna yabon Ubangiji!
3
“Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki! Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa; zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
4
“Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir, sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom, ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo, gizagizai sun zubo da ruwa.
5
Duwatsu suka girgizu a gaban Ubangiji, Wannan na Sinai, a gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.
6
“A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, an yashe dukan hanyoyi; matafiye suka bi hanyoyin da suka yi kona-kona.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options