Mahukunta 4:12-18
12
Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor,
13
sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.
14
Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi.
15
Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa.
16
Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira.
17
Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene.
18
Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo.
Settings