Skip to content
Mahukunta 20:35-48

Mahukunta 20:35-48

35
Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Benyamin a gaban Isra’ila; a ranar kuwa Isra’ilawa sun kashe mutum 25,100 na mutanen Benyamin, dukansu ɗauke da takuba.
36
Sa’an nan Benyamin suka ga an ci su. To, mutanen Isra’ila sun yi ta ja da baya daga mutanen Benyamin domin suna dogara ga waɗanda sa su yi kwanto kusa da Gibeya ne.
37
Mutanen da suke kwanto suka yi wuf suka ruga cikin Gibeya, suka bazu suka kuma karkashe dukan waɗanda suke a birnin.
38
Mutanen Isra’ila sun riga sun shirya da ’yan kwanton cewa su murtuke hayaƙi daga birnin,
39
a sa’an nan ne mutanen Isra’ila za su juya su fāɗa wa mutane Benyamin da yaƙi. Mutanen Benyamin sun fara karkashe mutum talatin na Isra’ila, sai suka ce, “Muna cin nasara a kansu kamar dā.”
40
Amma da alamar hayaƙi ya fara murtukewa daga birnin, sai mutanen Benyamin suka juya suka ga hayaƙi yana murtukewa ko’ina a cikin birnin zuwa sararin sama.
41
Sa’an nan mutanen Isra’ila suka juyo musu, mutanen Benyamin kuwa suka tsorata domin sun gane masifa ta zo musu.
42
Saboda haka suka tsere a gaban Isra’ila zuwa wajen hamada, amma ba su iya tsere wa yaƙin ba. Mutanen Isra’ila da suka fito daga cikin birnin suka karkashe su a can.
43
Suka kewaye mutanen Benyamin, suka kore su, suka fatattake su a wajajen Gibeya a gabashi.
44
Mutum dubu goma sha takwas na mutanen Benyamin suka mutu dukansu kuwa jarumai ne.
45
Da suka juya suka juya suka tsere zuwa wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, Isra’ilawa suka kashe mutum dubu biyar a kan hanyoyi. Suka yi ta matsa wa mutanen Benyamin har zuwa Gidom suka kashe mutum dubu biyu kuma.
46
A ranar kuwa mutanen Benyamin dubu ashirin da biyar ne aka kashe, dukansu jarumai.
47
Amma mutane ɗari shida suka juya suka tsere wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, inda suka zauna wata huɗu.
48
Mutanen Isra’ila suka koma wurin mutanen Benyamin suka kashe dukan waɗanda suke a birnin, tare da dabbobi da kome da suka samu. Dukan garuruwan da suka samu sun ƙone su ƙaf.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options