Mahukunta 19:10-15
10
Amma bai so ya sāke kwana a can ba, mutumin ya tashi ya tafi ya bi ta Yebus (wato, Urushalima), tare da jakunansa biyu da aka yi musu shimfiɗa da kuma ƙwarƙwaransa.
11
Sa’ad da suka yi kusa da Yebus dare kuma ya riga ya yi, bawan ya ce wa maigidansa, “Mu dakata a birnin nan na Yebusiyawa mu kwana.”
12
Maigidansa ya ce, “A’a. Ba za mu shiga birnin baƙi waɗanda mutanensu ba Isra’ilawa ba. Za mu ci gaba zuwa Gibeya.”
13
Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.”
14
Saboda haka suka ci gaba, rana tana fāɗuwa sa’ad da suka yi kusa da Gibeya a Benyamin.
15
A can suka dakata don su kwana, suka tafi suka zauna a dandali birnin, amma wani ya shigar da su gidansa da daren.
Settings