Mahukunta 16:23-27
23
To, sai Filistiyawa suka taru don su miƙa hadaya ga Dagon allahnsu su kuma yi biki cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu Samson a hannuwanmu.”
24
Sa’ad da mutane suka gan shi, sai suka yabi allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu a hannunmu, wanda ya lalace ƙasarmu ya kuma raɓanya kisan mutanenmu.”
25
Yayinda suke cikin farin ciki, sai suka yi ihu, suka ce, “Fito mana da Samson yă yi mana wasa.” Saboda haka aka zo da Samson daga kurkuku, shi kuwa ya yi wasa a gabansu. Sa’ad da suka tsai da shi a tsakanin ginshiƙai,
26
sai Samson ya ce wa bawan da ya riƙe hannunsa, “Ka kai ni inda zan taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da wannan haikali, don in jingina a kai.”
27
To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa.
Settings