Mahukunta 16:22-31
22
Amma gashi kansa ya fara tohuwa kuma bayan an aske shi.
23
To, sai Filistiyawa suka taru don su miƙa hadaya ga Dagon allahnsu su kuma yi biki cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu Samson a hannuwanmu.”
24
Sa’ad da mutane suka gan shi, sai suka yabi allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu a hannunmu, wanda ya lalace ƙasarmu ya kuma raɓanya kisan mutanenmu.”
25
Yayinda suke cikin farin ciki, sai suka yi ihu, suka ce, “Fito mana da Samson yă yi mana wasa.” Saboda haka aka zo da Samson daga kurkuku, shi kuwa ya yi wasa a gabansu. Sa’ad da suka tsai da shi a tsakanin ginshiƙai,
26
sai Samson ya ce wa bawan da ya riƙe hannunsa, “Ka kai ni inda zan taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da wannan haikali, don in jingina a kai.”
27
To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa.
28
Sa’an nan Samson ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ya Allah ka tuna da ni, ka ƙarfafa ni sau ɗaya nan kaɗai, ka bar ni da bugu ɗaya kawai in ɗauki fansa a kan Filistiyawa domin idanuna.”
29
Sa’an nan Samson ya kai hannuwansa ga ginshiƙan waɗanda haikalin yake a kai, ya jingina jikinsa, hannunsa dama yana a ɗaya, hannun hagu kuma na ɗayan,
30
Samson ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Sa’an nan da dukan ƙarfinsa ya tura haikali ya fāɗa a kan shugabanni da dukan mutanen da suke ciki. Ta haka ya kashe mutane da yawa fiye da yayinda yake da rai.
31
Sa’an nan ’yan’uwansa da dukan dangin mahaifinsa suka gangaro don su ɗauke shi. Suka kawo shi suka binne tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin Manowa mahaifinsa. Ya yi mulkin Isra’ila shekara ashirin.
Settings