Skip to content
Mahukunta 1:9-13

Mahukunta 1:9-13

9
Bayan wannan, mutanen Yahuda suka gangara suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, Negeb, da gindin tuddai a yammanci.
10
Suka ci gaba suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron (wadda dā ake kira Kiriyat Arba) suka kuma ci Sheshai, Ahiman da Talmai da yaƙi.
11
Daga nan kuma suka ci gaba suka yaƙi mutanen da suke zaune a Debir (da ake kira a dā Kiriyat Sefer).
12
Sai Kaleb ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat Sefer ya kuma ci ta da yaƙi, zan ba shi ’yata Aksa yă aura.”
13
Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb ya ci birnin, saboda haka Kaleb ya ba shi ’yarsa Aksa ya aura.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options