Yoshuwa 2:12-21
12
Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa
13
za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”
14
Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”
15
Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.
16
Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”
17
Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba
18
sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.
19
In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.
20
In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.”
21
Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar.
Settings