Yunana 2:2-7
2
Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.
3
Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.
4
Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’
5
Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.
6
Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.
7
“Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki.
Settings