Yohanna 15:18-25
18
“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.
19
Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
20
Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.
21
Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba.
22
Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu.
23
Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma.
24
Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana.
25
Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’
Settings