Yohanna 11:49-53
49
Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!
50
Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
51
Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,
52
ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.
53
Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
Settings