Yohanna 11:54-57
54
Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
55
Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa.
56
Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?”
57
Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.
Settings