Yohanna 10:22-39
22
Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa.
23
Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon,
24
sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”
25
Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.
26
Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
27
Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.
28
Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
29
Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.
30
Da ni da Uba ɗaya ne.”
31
Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi,
32
amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”
33
Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”
34
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?
35
Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’
36
to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’
37
In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.
38
Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.”
39
Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.
Settings