Skip to content
Yowel 3:9-16

Yowel 3:9-16

9
Ku yi shelar wannan ga al’ummai. Ku yi shirin yaƙi! Ku tā da jarumawa! Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari.
10
Ku bubbuge garemaninku su zama takuba da kuma laujenku su zama māsu. Bari raunana su ce, “Ni mai ƙarfi ne!”
11
Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare, ku tattaru a can. Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!
12
“Bari a tā da dukan al’ummai; bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat gama a can zan zauna in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.
13
Ku fito da lauje, gama girbi ya nuna. Ku zo, ku tattaka inabin, gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba, muguntarsu da girma take!”
14
Dubun dubbai suna a cikin kwarin yanke shawara! Gama ranar Ubangiji ta yi kusa a cikin kwarin yanke shawara.
15
Za a duhunta rana da wata, taurari kuma ba za su ba da haske ba.
16
Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options