Yowel 2:28-32
28
“Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi.
29
Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.
30
Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai da kuma a kan duniya, za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.
31
Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.
32
Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.
Settings