Ayuba 40:1-9
1
Ubangiji ya ce wa Ayuba,
2
“Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”
3
Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
4
“Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna.
5
Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”
6
Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,
7
“Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini.
8
“Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?
9
Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?
Settings