Skip to content
Ayuba 40:1-14

Ayuba 40:1-14

1
Ubangiji ya ce wa Ayuba,
2
“Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”
3
Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
4
“Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna.
5
Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”
6
Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,
7
“Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini.
8
“Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?
9
Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?
10
Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma, ka yafa daraja da muƙami.
11
Ka saki fushinka, ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi.
12
Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya.
13
Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.
14
Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options