Ayuba 4:12-21
12
“Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji.
13
Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.
14
Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.
15
Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi.
16
Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.
17
‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?
18
In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,
19
to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!
20
Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.
21
Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’
Settings