Ayuba 38:22-35
22
“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara
23
waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa?
24
Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?
25
Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa
26
don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki
27
don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can?
28
Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa?
29
Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai
30
lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare?
31
“Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?
32
Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?
33
Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?
34
“Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?
35
Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’
Settings