Skip to content
Irmiya 48:14-28

Irmiya 48:14-28

14
“Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’
15
Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.
16
“Fāɗuwar Mowab ta yi kusa; bala’inta zai auku nan da nan.
17
Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’
18
“Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.
19
Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’
20
An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab.
21
Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,
22
zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,
23
zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,
24
zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.
25
An karye ƙahon Mowab; an karye hannunta,” in ji Ubangiji.
26
“Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya.
27
Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba? Ba a kama shi cikin ɓarayi, har kaɗa kai na ba’a kike yi a duka sa’ad da kike magana game da shi?
28
Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu, ku da kuke zama a Mowab. Ku zama kamar kurciyar da take sheƙarta a bakin kogo.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options