Irmiya 41:11-18
11
Sa’ad da Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka ji dukan laifofin da Ishmayel ɗan Netaniya ya aikata,
12
sai suka kwashe dukan mutanensu suka tafi don su yaƙi Ishmayel ɗan Netaniya. Suka iske shi kusa da babban tafki a Gibeyon.
13
Sa’ad da dukan mutanen da suke tare da Ishmayel suka ga Yohanan ɗan Kareya da shugabannin sojojin da suke tare da shi, sai suka yi farin ciki.
14
Dukan mutanen da Ishmayel ya kame a Mizfa suka juya, suka tafi wurin Yohanan ɗan Kareya.
15
Amma Ishmayel ɗan Netaniya da mutanensa takwas suka tsere daga Yohanan suka gudu zuwa wurin Ammonawa.
16
Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon
17
Sai suka ci gaba, suka dakata a Gerut Kimham kusa da Betlehem a kan hanyarsu zuwa Masar
18
don su kuɓuce wa Babiloniyawa. Sun ji tsoronsu domin Ishmayel ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wanda sarkin Babilon ya naɗa gwamna a kan ƙasar.
Settings