Irmiya 4:19-31
19
Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.
20
Masifa kan masifa; dukan ƙasar ta zama kufai. Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa, mafakata ba zato.
21
Har yaushe zan dubi tutar yaƙi in kuma ji karar ƙaho?
22
“Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”
23
Na dubi duniya, na ga cewa marar siffa ce babu kome; sammai kuma, haskensu ya tafi.
24
Na dubi duwatsu, sai na ga suna makyarkyata; dukan tuddai kuwa suna lilo.
25
Na duba, sai na ga ba kowa; kowane tsuntsu a sarari da ya tsere.
26
Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada; dukan garuruwanta sun zama kufai a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa.
27
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.
28
Saboda haka duniya za tă yi kuka sammai a bisa kuma za su yi duhu, domin na yi magana kuma ba zan fasa ba, na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.”
29
Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki.
30
Me kike yi, ya wadda aka ragargaza? Me ya sa kika sanya mulufi kika sa kayan adon zinariya? Me ya sa kika sa wa idanunki tozali? Kin yi kwalliyarki a banza. Masoyanki sun bar ki; suna neman ranki.
31
Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari, kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi, tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina! Na suma; an ba da raina ga masu kisana.”
Settings