Irmiya 38:14-28
14
Sai Sarki Zedekiya ya aika a kawo Irmiya annabi, ya sa aka kawo shi a ƙofa ta uku ta haikalin Ubangiji. Sai sarki ya ce wa Irmiya, “Zan tambaye ka wani abu, kada ka ɓoye mini wani abu.”
15
Irmiya ya ce wa Zedekiya, “In na ba ka amsa, ba za ka kashe ni ba? Ko da na ba ka shawara, ba za ka saurare ni ba.”
16
Amma Sarki Zedekiya ya yi wannan rantsuwa a kaɗaice ga Irmiya cewa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya ba mu numfashi, ba zan kashe ka ko in ba da kai ga waɗanda suke neman ranka ba.”
17
Sa’an nan Irmiya ya ce wa Zedekiya, “Ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon, za a bar ka da rai ba za a kuma ƙone wannan birni ba; da kai da iyalinka za ku rayu.
18
Amma in ba ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon ba, za a ba da wannan birni ga Babiloniyawa za su kuma cinna mata wuta; kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba.’ ”
19
Sarki Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawan da suka tafi wurin Babiloniyawa, gama Babiloniyawa mai yiwuwa su ba da ni gare su su kuma wulaƙanta ni.”
20
Irmiya ya ce, “Ba za su ba da kai ba, ka yi biyayya ga Ubangiji ta wurin yin abin da na faɗa maka. Ta haka zai zama maka da amfani, za ka kuwa rayu.
21
Amma in ka ƙi miƙa wuya, ga abin da Ubangiji ya bayyana mini.
22
Za a fitar da dukan matan da suka ragu a fadan sarkin Yahuda wa hafsoshin sarkin Babilon. Waɗannan mata za su ce maka, “ ‘Sun ruɗe ka suka kuma rinjaye ka, waɗannan abokanka. Ƙafafunka sun nutse a cikin laka; abokanka sun yashe ka.’
23
“Za a kawo dukan matanka da ’ya’yanka wa Babiloniyawa. Kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba amma za su sa sarkin Babilon zai kama ka; za a kuma ƙone wannan birni.”
24
Sai Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan zance, in ba haka ba za ka mutu.
25
In fadawa suka ji cewa na yi magana da kai, suka kuma zo wurinka suka ce, ‘Faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da kuma abin da sarki ya faɗa maka; kada ka ɓoye mana, in ba haka za mu kashe ka,’
26
sai ka ce musu cewa, ‘Na roƙi sarki kada yă mai da ni gidan Yonatan in mutu a can.’ ”
27
Dukan fadawa kuwa suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi, ya kuma faɗa musu dukan abin da sarki ya umarce shi ya faɗa. Saboda haka ba su ƙara ce masa kome ba, gama ba wanda ya ji zance da suka yi da sarki.
28
Irmiya kuwa ya zauna a sansanin masu gadi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi. Ga yadda aka ci Urushalima,
Settings