Skip to content
Irmiya 38:1-6

Irmiya 38:1-6

1
Shefatiya ɗan Mattan, Gedaliya ɗan Fashhur, Yukal ɗan Shelemiya da Fashhur ɗan Malkiya ya ji abin da Irmiya yana faɗa wa dukan mutane sa’ad da ya ce,
2
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’
3
Kuma ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Tabbatacce za a ba da wannan birni ga sojojin sarkin Babilon, wanda zai ci shi.’ ”
4
Sai fadawa suka ce wa sarki, “Ya kamata a kashe wannan mutum. Yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran mutane, ta wurin abubuwan da yake faɗa musu. Wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan sai dai wahala.”
5
“Yana a hannuwanku” Sarki Zedekiya ya amsa. “Sarki ba zai iya yin kome ya hana ku ba.”
6
Saboda haka suka kama Irmiya suka sa a rijiyar da ba ruwa a ciki ta Malkiya, ɗan sarki, wadda take a sansanin matsara. Suka saukar da Irmiya cikin rijiyar da ba ruwa da igiya; babu ruwa a cikinta, sai laka, Irmiya ya nutse cikin laka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options