Skip to content
Irmiya 22:20-30

Irmiya 22:20-30

20
“Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka.
21
Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba.
22
Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka.
23
Kai da kake zama a ‘Lebanon,’ kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda!
24
“Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.
25
Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.
26
Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu.
27
Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”
28
Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?
29
Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa, ki ji maganar Ubangiji!
30
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options