Skip to content
Irmiya 19:5-15

Irmiya 19:5-15

5
Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba.
6
Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa.
7
“ ‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji.
8
Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa.
9
Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’
10
“Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba,
11
ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri.
12
Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet.
13
Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”
14
Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don yă yi annabci, ya tsaya a filin haikalin Ubangiji ya ce wa mutane duka,
15
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa wannan birni da ƙauyukan da suke kewayensa kowace masifar da na furta a kansu, domin sun yi taurinkai, ba su kuwa saurari maganata ba.’ ”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options