Yaƙub 2:1-9
1
’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.
2
A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,
3
in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”
4
ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?
5
Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
6
Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?
7
Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?
8
In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.
9
Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.
Settings