Ishaya 66:7-14
7
“Kafin naƙuda ya fara mata, ta haihu; kafin zafi ya zo mata, ta haifi ɗa.
8
Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan? Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya ko a haifi al’umma farat ɗaya? Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda sai ta haifi ’ya’yanta.
9
Zan kai mace har haihuwa in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji. “Zan rufe mahaihuwa sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.
10
“Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita, dukanku waɗanda kuke ƙaunarta; ku yi farin ciki matuƙa tare da ita, dukanku waɗanda kuke makoki a kanta.
11
Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi da nonon ta’aziyyarta; za ku sha sosai ku kuma ji daɗin yalwarta.”
12
Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Zan fadada salama gare ta kamar kogi, wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu; za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.
13
Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”
14
Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki za ku kuma haɓaka kamar ciyawa; za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa, amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.
Settings