Skip to content
Ishaya 45:18-25

Ishaya 45:18-25

18
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
19
Ban yi magana asirce ba, daga wani wuri a ƙasar duhu ba; ban faɗa wa zuriyar Yaƙub, ‘Ku neme ni a banza ba.’ Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi; na furta abin da yake daidai.
20
“Ku tattaru ku zo; ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai. Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo, waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.
21
Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni.
22
“Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani.
23
Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse.
24
Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’ ” Duk wanda ya yi fushi da shi zai zo wurinsa ya kuma sha kunya.
25
Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila za su sami adalci za su kuwa yi yabo.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options