Ceton Isra’ila na har abada
14
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kayayyakin Masar da hajar Kush, da waɗannan dogayen Sabenawa, za su ƙetaro zuwa wurinku za su kuma zama naku; za su bi bayanku, suna zuwa cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su roƙe ku, suna cewa, ‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani; babu wani allah.’ ”
15
Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka, Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.
16
Dukan masu yin gumaka za su sha kunya; za su fita da kunya gaba ɗaya.
17
Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila da madawwamin ceto; ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba, har abada.
Settings