Ishaya 32:1-8
1
Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.
2
Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska mafaka kuma daga hadari, kamar rafuffukan ruwa a hamada da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.
3
Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba, kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.
4
Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta, harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.
5
Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.
6
Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.
7
Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.
8
Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.
Settings