Ishaya 30:18-21
18
Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
19
Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.
20
Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.
21
Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”
Settings