Skip to content
Ishaya 28:14-22

Ishaya 28:14-22

14
Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.
15
Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”
16
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.
17
Zan mai da gaskiya igiyar gwaji adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin; ƙanƙara za tă share mafakarku, ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.
18
Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku.
19
A duk sa’ad da ya zo; ko da safiya, ko dare ko kuma da rana, zai yi ta ratsawa yana kwasanku.” Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana,
20
wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado, yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.
21
Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim, zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba, yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.
22
Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options