Skip to content
Ishaya 13:14-18

Ishaya 13:14-18

14
Kamar barewar da ake farautarta kamar tumaki marasa makiyayi, haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa, kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
15
Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
16
Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu; za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
17
Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya.
18
Bakkunansu za su kashe samari; ba za su ji tausayin jarirai ba ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options